YANZU-YANZU: Gwamna El-Rufai ya yi alkawarin biyan Fansho da Gratuti kafin wa’adinsa ya ƙare

Advertisements

Jihar Kaduna- Gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da naira miliyan ɗari tara da ashirin (N920m) domin biyan bashin haƙƙoƙin ƴan fansho da gratuti na ma’aikatan jihar. 
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sakatariyar hukumar fansho ta jihar Kaduna, Farfesa Salamatu Isah, ta fitar a ranar Laraba a Kaduna. Rahoton Jaridar The Guardian ya tabbatar da hakan.
Tace kuɗin sun shafi rukuni 54 na ma’aikatan jiha dana ƙananan da suka yo ritaya da waɗanda suka rasa ran su. Rahoton The Cable.
Ta kuma cigaba da bayyana cewa za a biya kuɗin ne da tsohon tsarin ”Defined Benefit Scheme (DBS)”. 
Sakatariyar ta kuma ƙara bayanin cewa ƴan fanshon na gwamnatin jihar da ma’aikata da suka yi ritaya zasu samu naira miliyan ɗari huɗu (N400m), yayin takwarorin su na ƙananan hukumomi za su samu naira miliyan ɗari biyar da ashirin (N520m) 
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like