Advertisements
Rahotannin da ke shigo mana yanzu haka sun tabbatar mana da cewa an ga jinjirin Watan Ramadan a garin Dumaturu jihar Yobe. Haka kuma an samu ganin watan a Katsina.
Hakazalika kuma wani rahoton ya ce an samu ganin watan a Yola jihar Adamawa. Sai dai har yanzu ba a samu sanarwa ba daga Fadar Sarkin Musulmi ba, Sa’ad Abubakar III.
Daga Usman Umar Katsina