Kungiyar JIBWIS ta roki Gwamnatin Tarayya ta samar da isasun takardun naira a kasa domin shiga Ramadan

Advertisements

Kungiyar musulumin ta ce karancin nairan na wahala da mutane musamman cikin Ramadan.
Atiku Abubakar ya yi kira ga al’ummar musulmi su yi wa kasa addu’a.
Bauchi – Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah reshen Jihar Bauchi, a ranar Juma’a, ta roki gwamnatin tarayya da ta samar da wadatattun takardun kudi lokacin watan Ramadan. 
Shugaban kwamitin Tafsir, masallacin JIBWIS na kasuwar shanu, Alhaji Hassan Gwani, shi ne ya yi rokon yayin bude karatun tafsirin azumin Ramadan na bana, rahoton The Punch.
Ya ce: ”Azumi ya sake zagayowa kuma kudaden da ake al’amuran yau da kullum ba sa samuwa wanda hakan ya jefa mutane cikin wahalar siyen abun da su ke da bukata.
 ”Idan gwamnatin tarayya na son a karbi wannan tsarin, ya kamata ta yawaita sabbin takardun kudi don mutane su samu na kashewa.”
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like