Hukumar DSS ta tabbatar da cewa wasu ‘yan Siyasa na shirin yin Zagon ƙasa wa Tinubu

Advertisements

Wasu yan siyasa na shirya wa Tinubu makarkashiya.
DSS ta tabbatar cewa wasu ne neman kafa gwamnatin wucin gadi gabanin ranar 29 ga watan Mayu.
Yan sandan na farin kaya sun ce ba za a amince da hakan ba a lokaci na dimokradiyya bayan an yi zabe.
FCT, Abuja – Hukumar yan sandan farin kaya, DSS, ta tabbatar cewa akwai wasu yan siyasa da ke da mugunyar nufi kafa gwamnatin wucin gadi a Najeriya, The Punch ta rahoto.
 Shugaba Muhammadu Buhari zai mika mulki ne ga zababben shugaban kasa Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.
Kakakin DSS ya tabbatar wasu yan siyasa na son kawo cikas ga mika mulki ga Tinubu Amma, wasu yan siyasa suna ta kira ga shugaban kasa kada ya rantsar da Tinubu, inda suke cewa zaben da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ta APC ya ce ba amintaciyya bane.
A cikin wata sanarwa da ya fitar da ranar Laraba, 29 ga wayan Maris, mai magana da yawun DSS, Peter Afunanya, ya ce yan sandan farin kayan sun tabbatar da yunkurin da wasu yan siyasa ke yi na hana Tinubu karbar mulki daga hannun Shugaba Buhari.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like