Advertisements
Babban bankin Nijeriya ya ce bankuna 10 kawai ya bawa lasisin aiki matsayin bankunan kan waya Babban bankin yace, bankunan kuma zasu iya aiki a matsayin ƙaramin bankin bada lamuni ga ƙananan sana’o’i a ƙasa Bankin yace, bankunan basu da ofisoshi da yawa kamar sauran bankuna, sai dai suna da manhajojin su, kuma duk doka ɗaya suke amfani da ita da sauran bankunan gargajiya.
Bankunan da ake amfani dasu a waya na cigaba da samun haɓaka a Najeriya, saboda yadda masu bankunan ke ci gaba da samar da kayan fasaha na zamani da suke warware matsalolin ƴan Najeriya wajen amsa da aika ƙudi.
Hakazalika domin a tabbatarwa a wannan ƙarni ba’a bar kowa a baya a harkar kuɗi na zamani ba, CBN ya bawa kamfanoni damar buɗe bankuna masu amfani da manhaja.