DOMIN AL’UMMA: Maganin ciwon hakuri kyauta ga masu bukata, yana aiki sosai

Advertisements

CIWON HAQORI
A sami itacen tumfafiya a dafa da Jar Kanwa a kuskura da dimin shi safe da yamma har kwana 3, hakora za a warke.
KOGON HAQORI
A dibi Audugar cikin kwallon Tumfafiya a dangwali Nonon ta kadan asa cikin kogon, a rika yin haka Lokaci-Lokaci, kogon zai cike, (amma fa akwai zafi).
TSUTSAR HAQORI
A tafasa saiwar Tumfafiya kuskura da dimin shi, sau 3 a rana kwana 2,
zaka rabu da Ita.
HAQORA MAI JINI
A dafa sassaken Tumfafiya da ganyen ta a sa gishiri kaɗan, a kuskura baki da dumi-dumi sau 3 a rana kwana 1 za ayi,
hakora za su daina Jini.
WARIN BAKI
A dafa furen Tumfafiya da kwallon ta idan ruwan ya huce asa abin wanke baki (Brush) ana wanke bakin bayan an ɗan guntsi ruwan kayi bankwana da doyin baki,
HASKEN HAQORA
A shanya furen Tumfafiya idan ya bushe a maida shi gari a hada shi da Alaf kadan, a ɗangwala da buroshi ko asuwaki a wanke baki, hakora za su yi fari tas.
DATTIN GORO KO HAYAQIN TABA
A dafa furen Tumfafiya da lemun tsami (Lime) a wanke baki dashi da abin wanke baki (Brush) dattin zai fita daga baki gaba daya).
Allah ta’alah yasa mudace domin neman samun hadadan maganin sai akira wannan ☎️2348067931917 Ko chat WhatsApp
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *