DA ƊUMI ƊUMI: EFCC ta kama wasu matasa 17 bisa zargin damfara ta intanet a Makurdi

Advertisements

Jami’an hukumar EFCC, shiyyar Makurdi, a ranar 1 ga Afrilu, 2023 sun kama wasu matasa goma sha bakwai da ake zargi da damfara ta kafar Intanet a Makurdi, jihar Benue.

Wadanda ake zargin dai sun hada da Emmanuel Ikechukwu, Agbo Lawrence, Emmanuel Victor, Joseph Adoyr Ameh, Olamide Timothy, Augestine Adalache, Izuka Justin, Boniface Dudoo, Udechukwu Benedict da Emmanuel Igbo.

Sauran sun hada da Favor Nwokdi, Christian Nwgia, George Maaki, Yina Terseem, Wilson Egwoba, Isaac Ukange da Precious Tseaa.

An kama su ne biyo bayan bayanan sirri da aka samu.

Advertisements

Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da wayoyin hannu, katunan ATM, kwamfutoci, Lexus RX330 da kuma motocin Toyota Camry.

Wadanda ake zargin sun yi bayani mai amfani kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su a gaban kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like