Advertisements
By jaridar Alfarma |
APC, reshen jihar Delta, ta kori mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege daga jam’iyyar saboda wasu munanan laifuka da ake zarginsa da aikatawa.
tsigewar ta sa na kunshe ne a cikin wata takarda mai kwanan watan 31 ga watan Maris, 2023, kuma mai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar na jiha, Ulebor Isaac, a madadin kwamitin zartaswa na jam’iyyar na Jiha.
Advertisements
A cewar wasikar, ɗaukacin shugabannin jam’iyyar sun yanke shawara tare da amincewa da korar Omo-Agege a matsayin dan jam’iyyar da kwamitin zartarwa na mazaɓar Orogun da karamar hukumar Ughelli ta Arewa su ka yi.
Wasikar ta ce, “Kuma bisa tanadin sashe na 21.2 (1) (II) (VII) 21.3 da 21.5 (g) na kundin dokokin jam’iyyar na 2022 (kamar yadda aka gyara) mun yanke shawara gaba daya tare da amincewa da korar Sanata Ovie Omo Agege a matsayin dan jam’iyyar.