Hukumar kwastom sun mika jabun takardun kudi har dalar Amurka miliyan 6 da suka kama ga EFCC

Advertisements

Hukumar kwastom a yayin da ta ke mika kudaden ga hukumar ta EFCC

Hukumar kwastom a Nijeriya (NSC) ta mika jabun takardun kudi dalar Amurka miliyan 6 da suka kama a kan iyakar Seme border ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC).

Shugaban hukumar kwastom na shiyyar Seme, Badagry, Comptroller Dera Nnadi, wanda ya gabatar da jawabi a wata tattaunawa da hukumar EFCC din domin mika kudaden ya bayyana cewa, “Bangaren Seme, a cikin watanni uku na shekarar 2023 ya samu nasarori masu yawa a bangaren yaki kan fasakwauri.

“Wasu nasarorin da aka samu a kan fasakwaurin sun hada da kama jabun takardun kudi dalar Amurka miliyan 6 wanda ya yi daidai da naira biliyan 2.763 in an canza a kan naira 460.52 wanda za mu mika ga hukumar EFCC a yau.” 

Advertisements

Ya ma yi amfani da taron wajen neman kara samun hadin kan hukumar ta EFCC da sauran hukumomin tsaro a yakin da ake yi da fasakwauri a shiyyar.

Kwamandan hukumar EFCC a shiyyar Legas, Michael Wetkas, ya tabbatarwa hukumar kwastom din cewa za su kara gudanar da bincike dangane da jabun takardun kudi dalar Amurka miliyan 6 da jami’ansu suka kama a shiyyar Seme border. 

Wetkas, wanda ya yi godiya ga hukumar kwastom saboda dadadden hadin kai da ke tsakanin hukumomin biyu, ya tabbatar masu da kara samun goyon baya a yakin da ake yi da cin hanci da sauran abubuwan da suka shafi rashawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like