CIKIN AZUMI: Yan ta’adda sun sace mutane 100 a jihohin Katsina da Zamfara

Advertisements

An bayyana cewa ‘yan ta’adda sun sace mutane 100 a cikin gonaki a wasu garuruwa da ke jihohin Zamfara da Katsina.
An ruwaito cewa mutane 80 wadanda mafi yawansu yara ne aka sace a wani gari a Zamfara, a yayin da mutane 20 su kuma aka sace a jihar Katsina.
An bayyana cewa ‘yan bindigar sun afka cikin garin Wanzamai ne, wanda gari ne da ke kan iyakar jihar Zamfara da Katsina, tare da kai wannan hari.
Wani mazaunin kauyen Wanzamai da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, Sani Wanzamai, ya shaidawa Daily Trust cewa sama da yara 80 daga kauyen Wanzamai aka sace da kuma wasu sama da 20 daga kauyen Kucheri a karamar hukumar Tsafe da ke jihar da kuma garin ‘Yan Kara da ke makwafciyarsu jihar Katsina su ma aka sace su.
Kamar yadda sashen Hausa na rediyon BBC ya bayyana kuma PREMIUM TIMES ta nakalto, rahotanni sun nuna cewa mafiyawancin yaran sun shiga daji ne su samo icce inda wasu kuma aka kama su a gonakinsu. 
“Muna zaune da misalin karfe 8 na safe sai muka samu labarin cewa wasu yaranmu da suka tafi neman icce da kuma wasu da suka tafi gyara gonakinsu ‘yan bindiga sun sace su.” Kamar yadda wani shugaban kauye wanda ba a bayyana sunansa ba ya shaida.
Da aka tambaya adadin ko mutane nawa aka sace, sai shugaban kauyen ya ce, “Tsakanin 80 da 100.”
“Ba za mu iya cewa ga adadin yawan wadanda abin ya shafa ba, amma muna kyautata zaton tsakanin 80 da 100. Mafi yawansu samari ne wasu kuma sun kai shekaru ashirin. Akwai wani dattijo wanda ya ke cikin shekaru hamsin. Akwai kuma saura. Amma mafi yawansu matasa ne maza da mata.” Kamar yadda ya bayyana.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like