A cikin watan Azumi, yan bindiga sun sake kashe mutane a yankin Birnin Gwari

Advertisements

An ce daga cikin waɗanda maharan suka kashe harda yan Bijilanti, sun sace wasu 20.
Har yanzun mahukunta ba su ce komai ba game da sabon harin.
Kaduna – ‘Yan bindiga sun halaka mutane 9, cikinsu har da jami’an tsaro na ƙungiyar Banga huɗu a ƙauyen Sabon Layi, ƙaramar hukumar Birnin Gwari, a jihar Kaduna.
 Jaridar Leadership ta rahoto cewa yan ta’addan masu yawa sun kutsa cikin ƙauyen kana suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi duk da ana cikin watan Azumi.
Bayanai sun nuna cewa yayin wannan kazamin hari, yan bindigan sun yi ajalin mutane 9, kana daga bisani suka yi awon gaba da wasu 20 da dabbobin al’umma. 
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like